Yau maulidinka maulana shehana tijani
Kafin nafara bege senakira ra.ufi
Ubangiji ta.ala dayatsarkake nazifi
Dafa i dajallabi banharshe yaqarakaifi
Narusa dushirin maqiya shehana tijani
Ya shehana tijani
E Allah kabanisa.aayabo nawanga Sufi
Kakauda hammu gammu sannan kabaniqarfi
Jininjiki nane ketafasa yarinqa zafi
Daga ankira masoyi auwalu marrasani
Ya shehana tijani
E Allahu kaisatin tafiyar dadikka qunci
Ga rasulu musdafal arabi arziqinsa munci
Ikirayi Alihi dasahabbai sunada yanci
Acikin yaban dazanso daaso naso nayoni
Yaumalidinka maulana shehana tijani
Barkadayau inakwana fadima karima
Meji dajin Muhammadu Lallai kinadagirma
Danai yaban ma.aikin Allah danaki kema
Yaugayabo gurin danki jinin rasulu aini
Ya shehana tijani
barhama daiman inyass baburan acanzo
Munrayune afaila wasucan abasu qanzo
Maulaya shak yahuza dafa.inmune kuzazzo
Na Zariyanmu me qadfaza kakauda rauni
Ya shehana tijani
Naisallama gakai maulana ayatijani
Qure Binciken Sanin masana kaisaninka rauni
Wazayasanka bayan Manzo qurratu aini
Kowa yasanka To yamantokane amini
Yaumalidinka maulana shehana tijani