Labarin Talakka da Attajirai – Kashi na 2
Bayan Ibrahim ya zama wakili (agenti), rayuwarsa ta fara canzawa. Mutane da yawa suka fara girmama shi saboda gaskiyarsa, mutuncinsa, da kuma taimakon da yake yi wa talakawa.
Duk wanda ya je wajensa da wata matsala, Ibrahim yana ƙoƙarin nemo masa mafita ba tare da son zuciya ba. Wannan ya sa sunansa ya bazu a duk ƙauyuka da ke kewaye.
Amma wasu attajirai da suka taɓa raina shi ba su ji daɗin wannan canji ba. Suka fara haɗuwa a ɓoye domin su shirya yadda za su ɓata masa suna.
Shugabansu ya ce:
«"Ba za mu bari talakka ya fi mu daraja ba. Dole ne mu sa mutane su daina yarda da shi."»
Bayan kwana biyu, suka shirya wata makarkashiya. Suka ɓoye wasu kuɗaɗe masu yawa, sannan suka yaɗa jita-jitar cewa Ibrahim ne ya sace su.
Labarin ya bazu cikin gari cikin sauri. Wasu mutane suka fara zargin Ibrahim, amma waɗanda suka san halinsa suka ce:
«"Ba zai taɓa yin sata ba. Ibrahim mutum ne mai gaskiya da amana."»
Saboda rikicin ya ƙara kamari, shugaban gari ya kira babban taro domin a binciki gaskiyar lamarin.
A ranar taron, talakawa da attajirai suka hallara. Kowa ya cika da mamaki da fargaba, yana jiran a ji abin da gaskiya za ta bayyana.
Ibrahim ya tsaya cikin kwanciyar hankali ya ce:
«"Ban taɓa ɗaukar abin da ba nawa ba. Ina da yaƙinin cewa gaskiya za ta bayyana, ko da bayan wani lokaci ne."»
Sai taron ya yi shiru, ana jiran a fara bincike.
A ci gaba...