[Intro - Female]
Ruwan zuma ko ruwan guba,
Ko ruwan jira,
Shi so ya yake ne?
[Verse 1 - Male]
Barshi, salam, ba testing ko gudaa daya,
Baya jira, so ba cuta balle zuma.
In ka ji testing, harshen naka ne haka,
Sarki so, gashi muna ta dandana.
Harshe ne daban-daban,
Mai tsami da mai guba,
Mai daci da mai zuma.
So baya cikin guba,
Sannan bai zama zuma,
Mu ke bashi gun zama,
Shi so bai da matsala,
Sirri ne na zuciya.
So ba ya zama guba,
Sannan bai cikin zuma,
Mu ke bashi gun zama,
Shi so bai da matsala,
Sirri ne na zuciya.
Komai sai dashi ake,
Duk mai rai ciki yake,
Ko aure da so ake,
Kowa nashi ya rike.
Nima sai dako nake,
Na kosa, ina kike?
Yarinya kira nake,
Ban hannun ki in rike.
Allah sarki zuciya ta,
Ba ta girma.
'Yammata ku zo ku ganta,
Za ku ganta 'yar budurwa,
Yara-yara ke ta nema,
A soyayya.
Kune burin zuciya ta,
Wace zata debe kewa?
Kuzo yara,
Mu dai-daita.
[Male - Melodic Section]
'Yar shila body dan kadan,
Ki bani dama nan da nan,
Da so da kauna za ki ban,
Zo yarinya 'yar chas da ke.
Aure nake so ni da ke,
Na fara wasa na da ke,
Da na shigo kofa rufe.
[Female]
Fara kala ko bakar kala,
Ko da jar kala,
Shi so ya yake ne?
Sarki so, nai nazarin shi kan ido,
Kullum bincike nake,
Neman ilimi nake,
Ko zan gane ya yake.
[Male]
Sarki so, shi yanayin gilashi yake,
Ba karko rago yake,
Karfi balla so yake,
Yankan so dafi yake.
Tamkar yau da ni da ke,
Ai bayan gilashi muke,
Gefe na daban da ke.
Kin san shi rago yake,
Ba ya jure farmaki,
Amma ya yi shamaki.
[Female]
Sarki so, yanzu na gane ya yake,
Can ka goge bangare,
Nan na goge bangare.
Mun dauke duhun dare,
Sannan so ya cancare.
In na barshi ya yi duhu,
Kai ma dole ka yi duhu,
Nai ma labulen buhu.
[Duet - Outro]
Kar mu yi labulen buhu.